Latest:
Labarai

Ƴan sanda sun musanta karkatar da kayan tallafin a Katsina

 

Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta bukaci al’umma da su yi watsi da wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta na zargin karkatar da kayan tallafin abinci da jami’anta ke yi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, PPRO, ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya fitar.

Rundunar ƴan sandan ta ce faifan bidiyon ba kawai yaudara ba ne, an fitar da shi ne da nufin bata sunan ƴansanda.

“Bayan cikakken bincike, an gano cewa buhunan shinkafar da aka gani a bidiyon a cikin motar ‘yan sanda an kama su ne daga hannun wasu ɓatagari.

“Wasu marasa gaskiya sun yi samu fiye da kason su na kayan agajin , shine ƴan sanda suka kama suka kuma mayar da su wurin da aka raba.

“Saboda haka abinda bidiyon ta nuna ba shi bane gaskiyar lamari kuma yunƙuri ne na kushe kyakkyawan ƙoƙarin jami’an da aka tura wurin don ba da tallafi, ɗaukar matakan tsaro da tabbatar da gudanar da taron lafiya,” in ji ‘yan sanda.

Rundunar ƴan sandan ta kuma tabbatar wa jama’a cewa zarge-zargen da aka yi a cikin wannan faifan bidiyo ƙarya ne.

Daily Nigerian Hausa

Leave a Reply