Jamiâar Kalaba ta cire Shugaban Tsangayar Aikin Lauya, Farfesa Cyril Ndifon daga matsayinsa tare da dakatar da shi daga aiki, saboda zargin da Éalibai mata ke masa na yin lalata da su.
Shugabar Jamiâar Farfesa Florence Obi ta kuma haramta wa lakcaran, wanda ya yi Æaurin suna kan lalata da Éalibai masu kananan shekaru, daga shiga harabar jamiâar, sai idan kwamitin binciken zargin da ake masa ne ya neme shi.
Kwamandan Boko Haram Da Ya kashe MayaÆa 82 Ya MiÆa Wuya
Karo na biyu ke nan daga shekarar 2015 da zargin lalata da Éalibai ya sa jamiâar ta dakatar da Cyril Ndifon, wanda shi ne Éan asalin Jihar Kuros Riba na farko da ya zama farfesa a fannin aikin lauya.
Sanarwar da Rajistaran jamiâar ya fitar ta ce an dakatar da Farfesa Cyril ne saboda zargin sa da saÉa dokokin jamiâar.
Dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar 18 ga Agusta 2023, bayan rashin gamsuwar Shugabar Jamiâar da bayanin Farfesa Cyril Ndifon game da zargin da Éaliban nasa mata ke masa.
A âyan kwanakin da suka wuce ne Éalibai mata daga Tsangayar Aikin Lauya ta jamiâar Éauke da kwalaye suka yi zanga-zangar neman a sallami Farfesa Ndifon bisa zargin sa da lalata da su.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








