Labarai

Ranar Dimokuraɗiyya: Dimokuraɗiyya a Najeriya tana halin ƙaƙanikayi cewar Atiku Abubakar 

 

A daidai lokacin da Najeriya ke bikin ranar Dimokuraɗiyya na shekara ta 2023, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yace dimokuraɗiyya a Najeriya tana halin ƙaƙanikayi kuma dole yan Najeriya sun haɗa karfi da karfe kafin a ceto ta.

Cikin wata sanarwar data fito ranar Lahadi, dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 25 ga watan Fabrairun shekara ta 2023 yace dole sai wadanda suke kan madafun iko sun daina tsoma baki a sakamakon zaɓe.

Atiku yace ranar dimokuraɗiyyar Najeriya rana ce da za’a auna tsayuwar kasar akan turbar dimokuraɗiyya.

Atiku ya kuma ce akwai sauran aiki a gaba domin farfado da Najeriya cikin hayyacinta na dimokuraɗiyya.

Leave a Reply